Spread the love

D

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

A yau ne wani jigo a jam’iyyar NRM mai Zuma Dakta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, ya yanke shawara ajiye jam’iyyar sa kuma ya dauki jam’iyyar APC wadda tsohon gwamna zamfara Alhaji Abdul Aziz yari Abubakar ke jagoranta.

Dactan ya fadi hakan ne lokacin da yake yiwa manema labarai bayani dalilin zuwan sa garin mafara domin ganawa da tsohon gwamna, yace babban dalilin da yasa ya yanke shawara na bin tsohon gwamna a siyasar sa shine , la’akari da irin gudunmuwa da ya bada bisa ga halin da zamfara ta tsinci kanta na ta barbarewar tsaro.

“Dan gane da matsalar tsaro lokacin mulkin sa nasan na kai shi kara a kotuna daban daban a fadin Duniyar nan, kai harda kotun dake shari’ar manyan laifuka ta Duniya na kai shi kara, amma daga baya sai na gano cewa abunda yake fadawa al’ummar sa gaskiyar magana kenan.

“Ganin haka yasa na yanke shawara in ba shi goyon baya, ga tafiyar siyasar sa, saboda haka kowa yasan ni badon neman abun Duniya nake yiba, sai dai don na lura da Abdul Aziz Yari Abubakar mutum ne mai fada da cikwa, gashi kuma yanada alkibla kamar wannan gwamnati mai ci yan zuba.” inji Dakta.
Dakta shinkafi haka kuma yayi tsokaci kan shirin sulhu da gwamnati mai ci yanzu keyi, inda yace wannan sulhun dodorido ne, saboda bai taba ganin inda aka yi sulhu irin na jihar zamfara ba.

“Ance ana sulhu tsakanin Fulani yan bindiga da sauran jama’ar jihar zamfara, amma abun ban mamaki da ban takaici idan aka kama dan sakai da bindiga ko kuma ya kai hari ga bafulatani, gwamnati zata kama shi ta hukun tashi.

” Amma idan bafulatani yakai hari, ko mutun nawa ya kashe babu wanda zai kama shi ballan tana ayi masa hukun ci, to kaga kenan wannan sulhun na da gyara kwarai da gaske. Gwamnati ta maida mutane yan baura da yan moya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *