Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya aminta da bayanan  kwamitin ganin wata a majalisarsa ya bayar na rashin ganin watan Rajab a jiya Assabar don haka ya aiyana gobe Litinin a matsayin 1 ga watan Sha’aban 1442 wadda ta yi daidai da 15 Maris 2021 hakan ke nuna wannan watan ya yi farilla kenan.

A bayanin da shugaban kwamitin harkokin addini a majalisar sarkin musulmi, kuma Waziri Farfesa Sambo Wali Junaidu ya fitar ya ce duk kwamitocin ganin wata a kasar Nijeriya an bincike su ba in da aka samu labarin ganin wata don haka ya zama yau Lahadi 30 ga watan Rajab 1442 bayan hijira.

Wanan bayanin ke nuna watan Azumin Ramadan ya karaso saura kwana 30 kenan ga wanda Allah ya kaddare shi ga ganin lokacin.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *