Spread the love

 

Duk da gwamnatin Buhari ta ce ba za ta kara kuɗin man fetur a watan Maris ba, sai gashi hukuma mai kula da farashin Man PPPRA ta sanya farashin kowace litar Mai kan 212.61.

Hukumar ta bayar da sanarwa ƙarin mai ne a daren jiya Alhamis cewa farashin man zai tsaya ne tsakanin ₦209.61 zuwa 212.61 ya danganta da farashin da Man ya shigo ƙasar Nijeriya.

A tsarin farashin Man a watan Maris PPRA ta ce yanda man zai sauka gare ta kan ₦189.61 bayan ta biya harajin hukumomi masu kula da harkokin man.

Hukumar NNPC ta faɗi a watan Fabarairu ba za a yi ƙarin farashin man a Maris za ta yi zama da ƙungiyar ƙwadago da masu ruwa da tsaki a samu bakin zaren da zai sa talaka ba zai shiga cikin wahala ba.

Ta yi kira ga ‘yan kasuwar Man kar su kawo ƙarancin Man na da gangan domin akawi mai a ƙasar daga nan har tsawon kwana 40.

Duk bayan waɗannan bayanai sai ga shi an yi ƙarin wanda hakan zai ƙara jefa talakan ƙasar nan cikin mawuyacin hali da tsadar rayuwa.

Ana murnar farashin mai ɗaga a kasuwar duniya talakan Nijeriya zai ji sauki sai a ƙara sanya shi cikin matsi da takura.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *