Spread the love

Mahara sun kashe mutum ɗaya sun raunata mutane da dama a wani hari da suka kai a jihar Neja.

Wannan karon maharan sun mamaye al’ummar Kapana a ƙaramar hukumar Munya dake jihar in da suka yi garkuwa da mutane 18.

Maharan sun shiga garin ne a Talata da dare kamar yadda suka saba na harbi kan mai uwa da wabi in suka shiga ƙauye.

Mutanen ƙauyukkan a wurin gudun tsira sun samu rauni daga cikinsu waɗanda ba su yi sa’a ba musamman mata da ƙananan yara an yi garkuwa da su a lokacin da suke ƙoƙarin guduwa.

Ƙauyen da lamarin ya faru sun watse zuwa maƙwabtansu, ɗan majalisar dokoki dake waƙiltar Munya Mista Andrew Danjuma Jagaba ya tabbatar da faruwar lamarin na ban takaici.

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta samar da jami’an tsaro a yankin gudun sake irin wannan mamaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *