Spread the love

Gidajen Malaman jami’a mallakar jihar Sakkwato tun sanda aka gina su tare da wuraren karatu da ɗakunan kwana na ɗalibbai aka buɗe makaranta don soma karatu ba a shiga cikin gidajen  ba har zuwa yau da Managarciya ta ziyarci makarantar domin ganin shirin da ake yi na bukin yaye ɗalibai da za a yi.

Gidajen malaman jami’ar da macizai suka mamaye

Gidajen an gina su da tsari mai kyau, gidan shugaban makaranta a daban yake, in da a gefe aka gina gidajen malamai 100, kowace katanga tana ɗauke da gida huɗu sama biyu ƙasa biyu, a farkon makaranta kuma aka samar gidajen ƙasa na  shugabannin kowace  tsangaya ta makarantar, gidajen gwanin ban shawa.

 

 

A yau kusan shekara takwas gwamnatin Sakkwato tabar gidajen ba kowa cikinsu a lokacin da malaman makarantar ke fita waje neman hayar gida da yawansu na buƙatar gidajen amma ba yanda za su yi sun sanya ido ga abin da yafi karfinsu.

A lokacin da Managarciya ta ziyarci gidajen ta samu sun cika da haki ta ko’ina wasu gambunansu sun ɓalle, ba komi gidajen sai macizai kamar yadda wata majiya ta tabbatar ganin yanda wani maciji ya tafi ya ɓoye a lokacin da manema labaran suke wurin.

Akwai sakaci sosai na gwamnatin jiha da ta bar gidajen hannun macizai da aljannu ta himmantu wurin kashe kuɗin yaye ɗalibbai a lokacin da malamai ke ƙorafin wurin shiga.

Da yawan mutane na mamakin yanda shugaban jami’ar ke zama a cikin gari ganin yanda zamansa a cikin makarantar yake da matuƙar muhimmanci.

Managarciya ta tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na makarantar Zayyanu Shehu don sanin dalilin da ya sanya har yanzu malamai ba su shiga cikin gidajen ba har macizai sun mamaye wuraren.

 

 

 

Jami’in ya ƙi ya yi magana kan lamarin don yana ganin manema labaran sun saɓa ƙa’idar aiki da neman bayani ga wanda abin ya shafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *