Daga Aminu Abdullahi Gusau.

 

A yau ne gwamnatin jihar Zamfara ta karɓi allurai dubu 55, 920 na rigakafin cutar mashako watau COVID 19.

Da yake duba allurar rigakafin a dakin ajiyar magunguna watau (Cold Room Central Store Samaru Gusau,) kwamishinan lafiya na jihar zamfara, Alhaji Yahaya Mohammed kanoma yace gwamnati zata jajirce domin taga ko wane dan kasa anyi masa wannan allurar rigakafin.

Ya bayyana cewa jimillar mutane 27,960 ne za su karbi alluran a jihar inda ya kara da cewa, za a yi allurar rigakafin ne tun daga yara ‘yan shekaru 18 zuwa sama a duk fadin jihar.

Kanoma ya kara cewa mutanen da za su fara karbar allurar rigakafin kwayar cutar za su kasance masu fada a jiya bayan an kammala yima gwamna da manyan mukarra ban gwamnati, daga nan sai ma’aikatan lafiya, sarakunan gargajiya, da masu sayar da man fetur ‘yan jarida da sauran su.

A cewarsa, a yanzu haka wasu likitocin suna karbar horo kan yadda za a ba da rigakafin da zarar an kammala horon za su fara aikinsu.

Kwamishinan ya kuma yaba wa UNICEF da WHO kan kokarin da suke yi na tabbatar da cewa allurar rigakafin ta isa jihohi daban daban, ya bayyana cewa irin rawar da suke takawa tanada muhimmanci ga gwamnati.

Ya ci gaba da bayanin cewa an yi kyakkyawan shiri don adana alluran ta hanyar tabbatar da wadatar ciyar wutar lantarki tare da kara dakunan sanyi masu awanni 24, tare da wutar lantarki da injunan samar da wutar lantarki guda biyu da kuma makamashin hasken rana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *