Spread the love

 

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Gwamnan Zamfara, Bello Muhammed Matawlle yaba ‘yan bindiga  da suka ƙi karɓar tayin sulhun da ake gudanarwa a jihar wa’adin wata biyu da su ajiye makamansu ko su haɗu da hushin hukuma, domin gwamnatin tarayya ta shirya tsab don ta karo jami’an soji har guda dubu shidda domin yakarsu.

Gwamnan yayi wannan bayani ne a a fadar gwamnati dake Gusau babban birnin jiha, lokacin da yake yiwa mutanen jihar Zamfara bayani dan gane da zaman da suka yi tare da shugaban kasa muhammadu Buhari inda yayi masa bayani irin abubuwan dake faruwa a Zamfara na ayukkan ‘yan ta’adda.

Yace abun bakin cikin da ya faru a garin jangebe, inda aka yi garkuwa da ‘yan matan makaranta hakika ya girgiza jama’ar wannan jihar, Najeriya da Duniya gaba daya.

“Wannan iftila’in ya dauki hankalin Duniya gaba daya na wane irin tsarin samar da tsaro ke akwai ga jihohin mu na arewacin Najeriya, inda matsalar tsaron sai karuwa takeyi kamar wutar daji, ya kama ta mu gwamnonin da abun ya shafa da mu kara dage wa mu yaki way an nan yan ta’adda.

“Mun samu nasarar karbo yaran na makarantar jangebe har su 279, kuma suna cikin koshin lafiya, kuma mun rigaya mun hadasu da uwayen su.

“Ta ban garen tattaunawar da muka yi da shugaba Buhari, da manyan jami’an tsaro a Abuja mun kai ƙarshen cewa za’a kara turomuna karin jami’an tsaro har dubu shidda domin su taimaka was wayanda kenan tare da mu”inji gwamna.

Matawalle ya ce nan ba da jimawa ba sojojin za su shigo Zamfara domin gudanar da ayukkansu. Ya kara da cewa satin da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta saka dokar hana sauka da tashin jiaragen zama da hakar zinari jihar Zamfara.

“Daga karshe shugaban kasa ya yarda da cewa yan ta’adda wayanda basu tuba suka bar ta’addanci ba da su gagguta yin hakan, kuma su ba da makaman su ga gwamnati.

Daga nan ne gwamna matawalle ya zaiyano irin nasarorin da suka samu tun lokacin da suka fara shirin sulhu, inda yace sun samu nasarar karbar makamai ga hannun tubabbun yan bindiga, da kuma kubutar da daruruwan mutanen da yan bindiga sukayi garkuwa dasu, an bude kasuwan ni da sauran kasuwan ci da kuma raguwar yawan kai hare hare ga mutanen da basu ji basu gani ba.

“Duk da wannan nasarar da muka samu ba zai hana mu kara daukan matakin da ya dace ba, domin muga mun kai karshen wannan abun gwamnati ta dauki wayan su makatai kamar haka.

Yan bindigar da basu taba ba, ambasu kwanan wata biyu dasu tuba,kuma su bada makaman su ga hukaumar da ya kamata.

“Yan siyasa su nisanta kansu dayin duk abunda zai kawo taɓarɓarewar tsaro, domin mun sanya jami’an tsaro su kula da abun da harkokin da yan siyasa ke yi, kuma duk wanda aka kama za’a dau kwakkwaran mataki a kansa.

“Mataki na ukku shi ne sarakuna da kantomomin kanana hukumomi su zauna a inda suke mulki domin kulawa da shige da ficen baki.Hakama mun hana daukar fiye da mutun daya saman Babur in kunne yaji gangar jiki ta tsira”.Inji matawalle.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *