Spread the love
Daga Muhammad M. Nasir
‘Yar rajin kare hakkin mata da kananan yara kuma ‘yar siyasa a jihar Sakkwato Barista Sa’adatu Muhammad Yanusa ta yi kira gwamnatocin kasar nan a kowane mataki da su fadaka su baiwa mata dama a hakokin siyasa da gwamnati.
Barista a bayanin da ta fitar  domin ranar mata da majalisar dunkin duniya ta ware ta taya mata murnar wannan ranar da fatan matan za su tashi tsaye a wurin nemawa kansu abin biyan bukata bisa hanyar da addini da al’ada suka aminta da ita.
Barista Sa’adatu ta ce lokaci ya yi da mata za su hada kansu wuri daya su nemawa kansu gurabu a harkokin siyasa musamman yanda aka barsu baya duk da suna iya tafiyar da jagoranci amma maza sun ki aminta da hakan.
A bayanin da Managarciya ta samu Barista ta ce a duk sanda mace ta fito neman wakilci sai ka ga an fara kallon ba za ta iya ba, a nuna mata karara wata ta aminta da hakan wata kuma ta jajirce duk da hakan sai an kulla  tuggun da za ta bari don kanta wanda hakan bai dace ba lokaci ya yi da yakamata a baiwa mata dama su gwada basira da tunanin da Allah ya ba su don bayar da gudunmuwar gina al’umma da kasa baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *