Spread the love

Farashin gangar Danyen Man fetur ya yi tashin gwauron zabo a karon farko cikin shekarar 2021 kowace ganga ana sayar da ita kan dala 71.28 a kasuwar duniya.

Wannan ya biyo bayan taron da kungiyar kasashe masu fitar da man a duniya suka yi na cijewa kan matsin da ake yi masu na su kara yawan man da suke fitarwa.

Masana harkar man sun yi hasashen a tsakiyar shekarar nan man zai daga zuwa dala 71, sai ga shi yanzu an wuce hasashensu.

Managarciya na ganin wannan gwamnatin ba ta da wani uzuri a yau da za ta gaywa talakan Nijeriya matukar ba ta inganta rayuwarsa ba, lokaci ya yi da zai samu saukin rayuwa a matsin da yake ciki.

Gwamnatin Buhari a lokacin da ta shigo farashin gangar man ta karye ana sayar da ita dala 28 ta yi ta kokawa kan halin da tattalin arzikin ya shiga yanzu ko da tattalin arzikin ya daga yakamata mutanen kasa su ga sauyi na alheri da cigaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *