Spread the love

Daga Muhammad M. Nasir

Sanannen malamin addini a Sakkwato Shaikh Abubakar Jibril  ya zargi Gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal da halin rashin cika alƙawali.

Malamin ya yi kalamansa a masallacin da yake bayar da Sallah ya ce babu wani alheri da za  a kira wani malami a ba shi ya baiwa wani ko ya kawo wani nasa  a bashi kwangila haka abubuwa ke tafiya a taɓarɓare a wannan gwamnatin Sakkwato.

“Ba mu san malaman da gwamnati ta aminta da su ba wannan matsalar ba za a  kyale ta ba mun san abin da yakamata mu yi mu ba dabbobi ba ne, duk wanda ya saɓa za mu faɗe shi.” a cewar Jibril

Ya ce Gwamnatin Sakkwato ta yanzu ba ta baiwa malamin addini muƙami ba,  a dubi wani dan siyasa a ce yafi shi mutunci a garin Sakkwato duk da shi ba da siyasa ya dogara ba, amma ya nuna rashin jindaɗinsa na hanawa ɗansa kujerar Kansila da ya nema tunda ya cancanta.

Ya ce Tambuwal ba ya faɗa da cikawa, ba a cewa mai gaskiya maƙaryaci shi ne zalunci  akawai buƙatar a gyara domin su ba wawaye ba ne ba makwaɗaita ba ne irin  kwaɗayin da zai jawo masu walaƙanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *