Daga M. A. Umar, Abuja.
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya taya matan Najeriya murnar zagayowar ranar mata ta duniya ta wannan shekarar.
Lawan ya bayyana taken bikin na wannan shekarar na “Zabin kalubale”, a matsayin abin da ya dace don tunatar da al’umma gaggarumar rawa da mata ke bayarwa a wajen gina iyali da kasa, da kuma bukatar a mai da hankali ga kalubalen da ke fuskantar su.
Ya ce mata suna taka rawar da ba a iya yi ba da su ba a rayuwar kashin kansu da ta jama’a, kuma sun bukaci dukkan goyon baya da girmamawar al’umma ga wannan rawar ta su.
Lawan yayi bayanin cewa mata sun cancanci dukkan goyon baya da kwarin gwiwa don su shiga a fafata da su ba tare da wata tsamgwama ko nuna bambamci a gudanar da harkar gwamnati da harkokin jama’a baki daya.
Mai baiwa shugaban majalisar, Ola Awoniyi ne ya bayyana sakon a wata takardar manema labarai da ya raba a yammacin lahadin nan, inda ya kara da cewar, shugaban majalisar Dakta Lawan ya bukaci da a rika yin tsari na jama’a da munufar samun kyakyawar gudummuwar mata don samun zaman lafiya da cigaban qasar mu.
Shugaban majalisar yace a ko wane lokaci majalisar dokoki ta tarayya a shirye take ta tabbatar da kare ‘yanci da muradun matan Najeriya, da kuma yaki da duk wani abu da zai yiwa jin dadin su da bukatun su shinge.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *