Spread the love

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya godewa tsohon gwamnan Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa da ya taya shi murnar cikarsa shekara 68 a duniya.

Sanata ya yi wannan godiyar ne a lokacin da mambobin ƙungiyar ‘yan jarida masu aika rahotanni a waje waton Correspondent chapel ta miƙa kyautar taya shi murna a gidansa dake Gawon Nama a birnin Sakkwato a wannan Assabar.

Wamakko ya ce “kafin ku zo ban da wata kyauta mai girma da aka yimin ta taya murnar ranar haihuwata saman ta Bafarawa amma yanzu ta ku ce kan gaba.” ya furta kalaman cikin farinciki da annashuwa.

Sanata bai ambato ko gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya taya shi ba, sai dai abin la’akari anan da ya taya shi zai furta kamar yadda ya faɗi kan Bafarawa.

Managarciya ta fahimci kyakkyawar alaƙa na ƙara ƙulluwa tsakanin jagororin siyasar guda biyu wanda hakan alheri ne ga siyasar jihar Sakkwato domin kaucewa adawa ta gaba da ƙiyayya a tsakanin magoya baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *