Spread the love
Shugaban Majalisar Dattijai ya jajantawa Majalisar Sarakunan Neja Kan Rashin Sarkin Kagara
Shugaban majalisar dattijai, Dakta Ahmad Lawan ya jajantawa al’ummar masarautar Kagara musamman gwamnatin Neja da tarayyar qasar nan bisa rasuwar mai martaba sarkin Kagara, Malam Salihu Tanko.
Shugaban ya bayyana cewar lallai rashin wannan dattijon basaraken babban rashi ne musamman duba da irin gudunmawar da ya bayar wajen cigaban al’umma ta fuskan zaman lafiya ba tare da nuna bambancin qabila ko addini ba wajen cigaban zaman lafiya da qaruwar arzikin qasar nan.
Bayanin hakan na qunshe ne a wata takardar manema labarai,  da mai taimakawa shugaban majalisar a vangaren labarai, Malam Salihu Inuwa Jibrin ya sanyawa hannu a yammacin alhamis xin nan.
Inda ya cigaba da cewar Dakta Lawan ya cigaba da cewar tabbatas majalisar sarakunan Neja, bisa jagorancin Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar ta rasa gwarzo wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen cigaban masarautun jihar duba da irin aqidunsa na son zaman lafiya ba tare da nuna bambanci tsakanin qabilun jihar da mabiya addinai a jihar ba.
Doktan ya jajantawa gwamnatin Neja, musamman majalisar sarakunan jihar bisa wannan babban rashin na xaya daga cikin sarakunan jihar, wanda yayi fatan Allah ya karbi baquncinsa ya gafarta mai kurakuransa, yasa aljanna ce makomarsa.
Da ya juya kan iyalan mamacin kuwa, yace su jure su yi haquri da wannan rashin domin rashi ne da ya shafi kowa da kowa, wanda ya bayyana cewar tarihi ba zai manta da irin gudunmawar da Malam Salihu Tanko ya bayar ba a lokacin rayuwarsa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *