Spread the love

Aminu Abdullahi Gusau

A yau ne gwamnatin jihar Zamfara ta musanta rahotannin wadan su kafafen yada labarai dake cewa ‘yan bindiga sun hallaka mutun arba’in a kauyen Ruwan Tofa dake karamar hukumar mulkin maru dake jihar ta Zamfara.

Da yake yiwa manema labarai bayani dangane da gaskiyar lamarin, gwamna matawalle yace abin da wasu kafafen yada labarai suka fada ba gaskiya ba ne, yace gaskiyar magana ita ce lokacin da mutanen kauyen suka samu labarin cewa ‘yan bindiga na kan hanyar su ta zuwa kauyen sai suka fito suka yi masu kwanton bauna inda suka halaka ‘yan bindiga da dama.
Gwamna wanda ya maganta ta bakin mataimakin shugaban ma’aikata na fadar gwamnati Dr, Bashir Muhammed Maru yace, bayan sun sha da kyar, sai suka sake wani sabon shiri suka dawo a wannan lokacin ne suka kara fafatawa da mutanen kauyen, inda suka kone motoci biyu dauke da kayan abinci, kuma suka sace kayan masarufi, da kuma yin garkuwa da wasu mutane wayanda yanzu haka an samu nasarar kubutar dasu.

Hakama ya bayyana cewa, wasu ‘yan jaridan ana amfani dasu ne domin biyan bukatun mutanen da basu son suga jihar Zamfara ta zauna lafiya. A don haka ya kara jan hankalin su dasu tantance labari ga hukumomin da abin ya shafa kafin su sanar da masu kallo ko sauraren su.

“Ina mamakin yadda mutun zai shige gidan sa, ya kama kiran kafafen yada labarai yana fada masu abinda ba yada tabbacin sa, domin dai yana son ya batawa gwamnatin mu suna, kuna ganin irin kokarin da muke yi wajen yin sulhu da yan’addan ga amma mun san wasu ba haka suke soba.”

Idan baku manta ba kwana biyu da sako ‘yan matan makarantar Jangebe, sai ga wani labari wanda BBC tayi hira da wani yana bayanin cewa ‘yan bindiga sun afkawa kauyen Tofa suka kashe mutun arba’in, suka kone motocin abinci, da shaguna kuma suka yi a won gaba da mutane domin a biya su kudin fansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *