Spread the love

Jama’atu Nasril Islam kungiya ce ta musulmai a Nijeriya ta ce ba za ta halarci mukabalar da aka shirya za a yi malamin addini Shaikh Abduljabar Nasir Kabara.

Mukabalar da aka shirya gudanarwa a ranar 7 ga watan Maris 2021 karkashin gwamnatin Kano a harabar masauratar Sarkin Kano.

Malamai da dama sun nuna rashin gamsuwarsu da karatun Kabara kuma suna ganin zagi ne da cin zarafin fiyayyen halitta Annabi Muhammad S. A. W.

Kungiyar tana karkashin Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubabakar a bayanin da sakatarenta Khalid Aliyu ya fitar sun tir da cin zagin Annabi da iyalansa da kuma sahabansa.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *