PDP ta bankado wani sirri da jam’iyar APC da gwamnatin tarayya ke yi na yunkurin sanya dokar ta baci a jihar Zamfara don haka jam’iyar ta yi jifa da wannan matakin na gurbata dimukuradiyya a jihar Zamfara bai kamata a daura laifin rashin samar da tsaro ga gwamna Bello Muhammad Matawalle ba kasawa ce ta jam’iyar APC wadda ita ce ke  jagorantar gwamnatin tarayya.

A bayanin da sakataren yada labarai na jam’iyar Kola Ologbodiyan ya fitar ya ce wannan shirin an fara shi ne tun sanda kotun koli ta ba shi nasara bayan an yi kokarin a mayar da shi APC ya ki aminta

PDP ta yi kira ga APC ta kyale gwamnan ya fuskanci aikin jama’a a wurin yakar ‘yan ta’adar musaman wadanda ke shigowa daga wasu wurare.

Jam’iyarmu ta tabbatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ke da alhakin kiyaye rayukkan jama’a ciki harda mutanen Zamfara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *