Spread the love

Kwamishinan matasa da bunkasa wasanni na jihar Sakkwato Bashir Gorau ya sanar cewa, “Da misalin karfe 12:45 na safe ne ’yan bindiga suka kai hari gidanmu da ke Garin Gorau, Karamar Hukumar Goronyo suka tafi da matar babban yayanmu Alhaji Lawali Gorau da wani dan uwanmu Hassan Manya.

Ya ce ‘yan bindigar sun shhigo garin suna harbin kan mai uwa da wabi suka dauki mutanen amma ba su jiwa kowa ciwo ba suka bar garin.

Ya ce har zuwa yanzu mutanen ba su tuntube su ba suna fatar ‘yan uwan nasu su dawo cikin koshin lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *