Spread the love

 

Tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya kaddamar da gadar sama Rumuogba 1, 2 a Fatakawal jihar Rivers wadda Gwamna Nyesom Wike ya gina ita ce mafi girma a jihar.

Sanata Kwankwaso a wurin bude aikin ya yi  kalamai masu nuna sabuwar alakar za ta daure ne har  2023 ya ce “muna sonka domin ka gudanar da aiki a jihar Rivers, saura shekara biyu ka kammala mulki a matsyin gwamna da ikon Allah za ka tafi sama domin aikin kasa.” a cewar Kwankwaso.

Wannan shaguben nasa yana nuni ne da cewar za su yi tafiya tare a siyasa mai zuwa da yake fatan samun nasara a tare da Wike “muna girmamaka yadda ka samar da zaman lafiya a jiha.

“Da aka gayyace ni na bude wannan gadar sama mai tsawon gaske da take da tarihi. Gwamna muna girmamaka domin an gani a kasa ka yi aiki a lokacin da wasu gwamnoni a jihohinsu sun yi batan dabo ka cigaba aiki ka cigaba tafiya da abubuwa masu kyau, zamanka gwamna ba karamin abu ba ne yarjejeniya ce tsakaninka da mutanenka domin a samar musu da romon dimukuradiyya.” Kalaman kwankwaso.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *