Sakataren Gwamnatin Neja Ta Jajanwa Al’umma Kan Rashin Sarkin Kagara
Daga M. A. Umar, Minna
Sakataren gwamnatin Neja, Ahmed Ibrahim Matane ya bayyana kaɗuwa da jajantawa kan rasuwar sarkin Kagara, Malam Salihu Tanko, wanda ya rasu yau a garin Kagara cikin ƙaramar hukumar Rafi.
Sarkin ya rasu yau talata bayan doguwar jinyar da yayi fama da ita.
Ahmed Matane ya bayyana sarkin a matsayin tsanin zaman lafiyar da ya shafi dukkanin ɓangaren rayuwa, wanda ya kawo cigaba da hadin kan al’umma ba tare da nuna bambancin addini ko harshe ba a dukkanin jihar.
A cewar sakataren gwamnatin, gudunmawar da marigayin ya bayar ya taimaka wajen cigaban masarautar Kagara da jihar baki ɗaya, da kuma Najeriya.
Rayuwarsa ta zama abin koyi domin cigaban da ya samar ta shafi dukkan komai wanda ya taimakawa dinbin al’umma.
A madadin gwamnatin jiha da al’ummar jihar baki ɗaya, ina son gabatar da jaje ga shugaban majalisar sarakunan jiha, mai martaba Etsu-Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar da iyalan marigayi Malam Salihu Tanko da al’ummar masarautar Kagara.
Ahmed Matane yayi addu’ar Allah ( SWT) ya gafartawa mamacin kurakuransa kuma ya ribanya mai lada a ayyukansa na alheri, ya kuma baiwa ‘yan uwa da abokan arziki hakurin rashin sa.
Sakataren ya bayyana cewar karfe hudun yammacin nan za a gudanar da jana’izarsa a garin Kagara hedikwatan ƙaramar hukumar Rafi da misalin karfe hudun yammacin nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *