Spread the love

Ɗaliban Zamfara Sun dawo gida  cikin ƙoshin lafiya

Daga Aminu Abdullahi Gusau

A cikin daren jiya Litinin daliban da aka dauke a garin jangebe dake karamar hukumar Talatar mafara a jihar Zamfara suka dawo gida su 274,

Da yake yiwa manema labari bayani gwamna matawalle yace yaran na cikin koshin lafiya, kuma da zarar an kammala duba lafiyar su za’a hannunta su ga uwayen su.

Gwamnan yace sunyi amfani da yan bindigar da suka tuba wajen karbo yaran kuma babu wasu kudi da aka biya domin sako su, ya kara jadda shirin sa na yin sulhu ganin cewa sulhu shine mafita ga wannan rashin tsaron da ya addabi jihar zamfara da Najeriya baki daya.

Yanzu dai daliban suna cikin gidan gwamnatin jihar zamfara, idan ba mantaba tun cikin daren juma’a akayi garkuwa dasu.

Hamaka gwamna yace daliban su 274 ne ba kamar yanda wasu kafafen yada labarai ke fada ba na cewa yaran dari ukku da kari ne. Hakama ya yi kira ga uwayen yaran dasu dauki wannan abun a matsayin kaddara.

Daya daga cikin daliban wadda ta zanta da manema labari tace sun sha wahala kwarai da gaske, inda tace a cikin kashi da fitsari suke zaune.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *