Spread the love

‘Yan ta’adda ɗauke da bindigogi sun kai hari a garin Amarawa cikin karamar hukunar Illela har sun kashe mutum 11 sun yi garkuwa da ɗaya a daren jiya Lahadi.

A cewar wata majiya da ke garin ta ce ‘yan ta’addar sun shigo garin suna ta harbe harbe kan mai uwa da wabi a kan hanyar gidan Alhaji Rabi’u wani dan kasuwa ne a kauyen da asubar jiya wanda shi ne suke son su sace.

A karon farko da suka ɗauke shi mutanen gari ba su bari aka tafi da shi ba, bayan dare ya raba kusan uku na daren jiya suka sake dawowa suka dauke shi mutanen garin suka bi su da nufin ceto shi kamar yadda suka yi a baya.

Da maharan suka fahimci akwai matsala suka cinnawa ƙauyen wuta abin da ya ba su damar kashe mutum 9 suka yi wa biyu yankan rago.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ASP Sanusi Abubakar ya tabbayar da kai harin  jami’an tsaro a jihar sun kara daure damara domin yakar mahara a yankin Illela, Goronyo, Sabon birni da Rabah har sai an dawo da zaman lafiya a yankin.

Ya yi kira ga mutanen gari su baiwa jami’an tsaro haɗin kai don dawo da zaman lafiya a yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *