Spread the love

Sabon farashin man fetur 170 ko 175 akwai yiwuwar gwamnatin Nijeriya za ta amince da shi a satin nan.

Kamfanin man fetur na kasa NNPC dake shigo da man da aka tace daga waje har yanzu ba ta kara kudin sayar da man ga matatu ba tsohon farashin ne na 158.33 har zuwa ranar Assabar data gabata, amma wasu jami’an gwamnati da ‘yan kasuwa sun tabbatarwa jaridar daily trust a wannan satin sabon farashin Man zai soma.

Ministan Man fetur a sati biyu  da suka  gabata ya ce ‘yan Nijeriya su shiryawa karin kudin man fetur ganin yanda gangar danyen man fetur ta yi sama a duniya ana sayar da kowace daya kan dala 60.

Dagawar danyen man fetur hakan zai sa kowace lita kudin kawota a Nijeriya  ta kama 180.

Duk da haka dai kamfanin NNPC ya fitar da sanarwa ta hannun mai magana da yawunsa Dakta Kennie ba maganar kari a yanzu za su zauna da kungiyar kwadago don samar da wata matsaya da ba za ta jefa talaka cikin wahala ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *