Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatarwa mutanen kasar Nijeriya satar yara ‘yan makaranta da aka yi a Jangebe shi ne zai zama na karshe hakan ba za ta sake faruwa ba.

Wannan bayanin na shugaban kasa ya fito a ranar Lahadi ta hannun ministan harkokin jiragen sama Sanata Hadi Sirika a lokacin da ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya wurin jajantawa gwamnati da mutanen  jihar Zamfara.

Ya ce sabbin matakai ana kan daukarsu domin kawo karshen aiyukkan ta’addanci a kasar Nijeriya.

Shugaban kasa ya nuna bacin ransa ga wannan satar da aka yi na daukar yara mata a sikandaren gwamnati za a tabbatar da gano ‘yan ta’adar a hukunta su.

Buhari ya yabawa gwamnan Zamfara a kokarin da yake yi na kawo karshen aiyukkan batagari a jihar.

A cikin tawagar akwai minintan ‘yan sanda Muhammad Maigari Dingyadi da Ministan jinkan jama’a Hajiya Sadiya Faruk da ministar mata mista Pauline  Tallen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *