Mawakiyar zamani Hairat Abdullahi wadda ta yi wakar Rariya da Mansur da Ruwan dare ta bayyana kanta a fili domin masoyanta da masu bibiyar wakarta su santa

A wata fira da ta yi da gidan rediyon BBC ta fadi sanda ta fara waka a masana’antar shirya finafinnai ta Kannywood “na fara wakar a 2013”. Hakan ya nuna sai bayan shekara shidda da fara yin wakarta sannan shahara ta zo mata kowane lamari akan so nacewa a cikinsa kafin samun nasara.

Hairat ta ce abin da ke da  wahala a waka samar da karinta da yanda za ka samar da bayaninta da zai dace da sakon da kake son ka isar.

Masoyiya wakar Indiya ce wanda take ganin hakan ya sanya ta zama mawakiya a harshen Hausa duk ba shi ne a salin yarenta ba “Ina son sauraren wakar Indiya sosai ina son wakokin Indiya.” a cewata.

Tana jin harsuna biyar da suka hada Eggon asalin harshenta da Hausa da Larabci da Indiya da Turanci, kuma ba ta da burin da ya wuce ta yi aure.

Ko kina shan wani abu ne muryaki take da zaƙi haka? ta ce bana shan komi ban da ruwa da shayi mai madara, waƙar da aka fara sanina da ita ce wakar ‘abin da ke raina zan fadi na huce takaici….’

Hairat ta yi ta mamakin yanda wasu in sun ganta aka ce ita ce ta yi waƙa ka za sai su musunta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *