Spread the love

Majisar sarakunan Zamfara sun jajantawa gwamnati da uwayen yaran da aka sace

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Manyan sarakunan jihar Zamfara karkashin jagorancin mai martaba Sarkin mafaran Anka Alhaji Attahiru Ahmed, sun jajantawa gwamnatin Matawalle da uwayen yara ‘yan makarantar kwana dake jangebe.

Ya ce sun zo a fadar gwamnati ne domin su nuna rashin jin daɗin su bisa ga abin da ya faru, inda yace a matsayin su na uwayen al’umma ya zama wajibi gare su da su jajanta bisa ga wannan iftila’i.

Sarkin Anka ya baiwa gwamna  shawarar cewa kada ya samu damuwa domin duk Duniya ta sheda irin ƙoƙarin da yake yi na ganin ya kawo zaman lafiya a fadin jihar ta Zamfara.

Ya ƙara da cewa, da yardar Allah nan gaba kadan Allah zai tona asirin wadanda ba su son zaman lafiyar kasar nan.

Sarkin Anka ya ce idan har kasawa ne ta bangaren tsaro, to gwamnatin tarayya ke da alhakin haka.

“Muna jajantawa uwayen yaran da aka sace, kuma muna nan muna ta addu’a domin muga an ceto wadan nan yaran”.

Da yake maida jawabi ,gwamna matawalle yace tsarinsa na sulhu shi ne abinda za’aci gaba da shi, har lokacin da aka kai ƙarshen matsalar tsaron.

Gwamnan ya ce sun samu labarai da dama wanda insha Allahu da zarar angano yaran zasu tona asirin abinda ke ciki.

Ya kuma ja hankalin jama’a da su ci gaba da yin addu’a domin samun kuɓutar da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *