Fargaba ta karu a jam’iyar PDP rikicin Secondus da ‘yan majalisarsa ya kara kamari

Jagororin siyasa a jam’iyar PDP daga Arewa suna ta fadi tashin ganin gwamnonin jam’iyar daga kudu maso kudu bukatarsu ba ta biya ba kan cire shugaban jam’iyar Secodus.

Shugaban jam’iyar PDP na kasa Yarima Uche Secondus yana ta iyakar kokarinsa shi da magoya bayansa ya rike mukaminsa da wasu jagororin jam’iyar ke son ganin bayansa.

Jagororin jam’iyar PDP sun rabu biyu kan shugaban wasu na ganin bai kamata ya cigaba da rike jam’iyar ba ganin yanda ya yi sama da fadi da kudin jam’iyar a binciken da aka yi na 2020 kuma ba ya da wata basirar da yake iya kai PDP ga nasara a zaben 2023, bayan samun rahoton binciken ne aka yi yunkurin tsige shugaban a Abuja abin da ba a yi nasara ba.

Manema labarai sun gano yunkurin wani shiri ne daga wani gwamna da ba ya kama bakinsa daga Kudu maso kudun abin da jagororin siyasa daga Arewa suka hana  don a fahimtarsu wannan zai hanawa jam’iyar ta su zaman lafiya.

Duk da hakan har yanzu wadanda ba su son ya cigaba da jagorancin jam’iyar suna da matukar karfi a cikin mambobin jam’iyar ba su kuma saduda ba.

Wata majiyar ta ce taron da aka kira a Abuja mambobin majalisar gudanarwar jam’iyar(NWC) a fili sun fito sun bayyana kasawar shugaban wanda bai dace ya cigaba da jagorancin jam’iyar ba. Zaman da aka kira domin tattauna abubuwan jam’iya bai kammala ba domin masu korafin ba a gamsar da su ba har kowa ya kama gabansa.

Magoya bayan shugaban sun ce komi ya wuce domin duk wadanda ke korafi an yi masu bayani gamsasshe kan korafinsu, sai dai in da wata manufa suke yi za su ci gaba.

Da yawan gwamnoni a jam’iyar suna ganin yakamata a mayar da yuka kube zuwa watan Disamban 2021 da wa’adin majalisar gudanarwar za ta kammala.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *