Spread the love
PDP ta nemi a saki Salisu Yakasai ba tare da kowane sharaɗi ba
PDP ta nemi  a gaggauta sakin Salisu Yakasai ɗa ga dattijon ƙasa Tanko Yakasai kuma jami’in yaɗa labarai na gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje  daga in da jami’an tsaro suke tsare da shi.
Jam’iyar a wani bayani da ta fitar wanda sakataren yaɗa labaranta Kola Ologbondiyan ya sanyawa hannu ya ce labarin kama Salisu da tsare shi wani wuri na sirri saboda ya yi suka ga kasawar gwamnatin Buhari wurin yaƙar ‘yan ta’adda a ƙasa, hakan ba abin amincewa ba ne.
Salisu ya tunatar da wani ɗan gwagwarmaya da yake sukar kasawar gwamnatin Buhari Abubakar Idris da an ka fi sani da Abu Hanifa Dadiyata tun a shekarar 2019 abin baƙinciki ya faru da shi har yanzu ba a san in da yake ba.
Ya ce PDP ta yi tir da wannan kamen don kawai Salisu ya goyi bayan masu kishin ƙasa da ke buƙatar fadar shugaban ƙasa ta yi tsaye a ƙwato yaran da aka sace a Zamfara.
PDP ta yi kira ga ‘ yan Nijeriya su ɗaura laifin abubuwan da ke faruwa kan gwamnatin APC rashin kyautawa ne a riƙa kama masu faɗin albarkacin bakinsu kan abin da ke faruwa a ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *