Mahara masu ta’addaci da garkuwa da mutane suna cin karensu ba babbaka a wasu dazuzzuka da a ciki ne suke shirya  ƙaddamar kai farmaki da ajiye mutanen da suka yi garkuwa da su.

Mutanen gari suna kalon dazuzzukan a matsayin gidan mutuwa, don yana da wahalar gaske jami’in tsaro ya je wurin.

Dajin guda Tara da suka haɗa da Sambisa da Alagarno da Kamuku da Kuduru da Kuyambana da Burwaye.

Sauran su ne dajin Ajja da Dajin Rugu da Sububu.

Waɗan nan wuraren sun zama ƙuncin mahara da ‘yan boko haram ba wanda  ke zuwa wuraren sai su da aminansu.

Masana sun hasashe matuƙar gwamnati ba ta karɓi dazuzzukan ba aka kori ‘yan ta’adda ba za a iya magance matsalar tsaro da ake fama da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *