Spread the love
Nijeriya za ta katse wutar da ta baiwa ƙasar Nijar da Benin kan bashin biliyan 2.60 da take biyarsu
Akwai yiwuwar Nijeriya za ta katse wutar da ta baiwa ƙasar jamhuriyar Nijar da Brnin kan bashin biliyan 2.60 da take binsu.
Bayanan bashin kuɗin wutar da ake bin ƙasashen yana ƙunshe ne a hukumar rarraba wuta ta ƙasa tun daga yanki na biyu na shekarar 2020 rahoton da aka fiyar jiya ya nuna hakan.
Gwamnatin tarayya a watan Disamban 2019 ta yi barazanar yanke wutar Togo a ƙasar Benin da Nijar kan ƙin biyan kuɗin wutar ga Nijeriya.
Kamar yadda tsarin hukamar yake duk wanda bai biya kuɗin wutarsa ba za a yanke ta haka abin yake kamar yadda tsohon darakta Usman Muhammad ya bayyana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *