Spread the love

 

Daga Ibrahim Hamisu.

Majalisar dokokin jihar Kano ta kafa kwamiti da zai binciki korafe-korafen al’umma kan zargin da ake yi wa kamfanin rarraba wutar lantarki (KEDCO) na gaza biyan bukatun al’ummar jihar.

Majalisar ƙarƙashin jagorancin shugaban ta Hamisu Ibrahim Chidari ta amince da kafa kwamitin ne a ranar Laraba, inda ta baiwa kwamitin makonni biyu domin miƙa rahotansu ga majalisar.

Ɗan majalisa mai waƙiltar karamar hukumar Ungogo Aminu Sa’ad Ungogo ne ya gabatar da kudurin gaggawa gaban zauren majalisar.

Ya ce lallai abin takaici ne yadda kamfanin na KEDCO ke gudanar da ayyukansa musamman wajen yin halin ko in kula ga jama’a ta fuskar samar da hasken wutar lantarki a jihar nan.

Sannan ya ce kamfanin yana yin wasa da koke-koken jama’a wajen gyara musu kayayyakin da su ke bayar da hasken wutar lantarki.

Kafin haka al’ummar jihar sun daɗe suna koka yadda bayar da wutar lantarki ke tafiya a jihar Kano.

Kamfanin baya iya ɗaga wa mutane a wurin biyan kuɗin wutar ko da ba su sha wutar ba, waton sun yi ta biyan kuɗin duhu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *