Spread the love
 Mahara sun sace ɗalibai mata a Jihar Zamfara
Wasu mahara sun sace ɗalibai mata na makarantar sakandaren Jangebe, dake ƙaramar hukumar Talata Mafara a jihar Zamfara.
 An  sace ɗaliban ne a daren ranar Juma’a, Sadi Kawaye, ya ce  har da ‘ya’yansa biyu mata, Mansura da Sakina daga cikin wanda ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su.
“Yanzu haka ina kan hanyata ta zuwa Jangebe don ganewa idona abin da ya faru, saboda an shaida min sun shiga makarantar da misalin ƙarfe 1 na dare”.
Kakakin ‘yansandan  jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu bai ce komai kan faruwar harin ba.
“Ka bani lokaci, yanzu ba zan iya cewa komai ba”, cewarsa
Satar yaran makaranta ta fara yawaita a Arewacin Nijeriya abin da ke nuna maharan na amfana da wannan ta’asar, bai fi sati da gurkwa da ɗalibban Kagara ba sai ga wannan a Zamfara .
Akwai buƙatar gwamnati ta tashi tsaye ga wannan ta’asar donin dawo da nutsuwa a cikin al’mma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *