Spread the love

 

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

A yau ne gwamna matawalle na jihar Zamfara ya ba da umurnin rufe makarantun kwana na boko a duk faɗin jihar Zamfara.

Wannan ya biyo bayan sace wasu ɗalibai mata a kusan 317 a makarantar mata dake garin Jangebe ƙaramar hukumar mulkin Talatar Mafara, da safiyar yau jumu’a.

Matawalle ya ba da wannan umurni jim kaɗan bayan da ya karɓi mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar 111. Domin jajanta mashi bisa ga sace ɗalibban.

Ya ce rufe makarantun ya zama wajibi kafin aga abunda zai faru nan bada jimawa ba, game da ‘yan matan makarantar Jangebe.

Hakama ya ce, yanzu haka an baza jami’an tsaro lungu da saƙo a wannan yankin domin a ceto yan makarantar ga hannun miyagun mutane.

Matawalle ya kara da cewa, gwamnatin tarayya ta kawo jiragen yaki da kuma ƙarin jami’an tsaro domin su taimaka wa waɗanda ke akwai wajen wannan aikin.

Idan baku manta ba, gwamnatin jihar Zamfara tana iya kokarin ta na ganin an yi sulhu da fulanin daji masu rike da makamai, inda yin hakan ya sa aka samu wasunsu suka ajiye makaman su suka rungumi zaman lafiya.

Daga cikin su akwai lawal Daudawa wanda ya bada bindiga kirar Ak 47 guda 18, da Ak 49 guda 2, da kuma dubban albarussai.

Haka zalika jiya Alhamis dan gidan Buharin Daji ya mika nashi makaman, har guda 30 da kari, domin shima ya rungumi zaman lafiya a jihar ta Zamfara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *