Maganin sauro ya kashe mutum 6 ’yan gida ɗaya a Kano
Wutar gobara ta tashi a wani gida dake unguwar Na’ibawa ‘Yanlemo a ƙaramar hukumar Kumbotso ta Jihar Kano ta yi sanadin mutuwar mutum  shida a gida ɗaya.
Mutanen unguwar sun zargi maganin sauro da aka kunna a gidan ne ya haddasa gobarar yayin da mutanen gidan suke tsaka da barci
Shaidun gani da ido sun cewa gobarar ta gidan Malam Abdurrahman Babawo ta yi ajalin mahaifiyarsa da ’ya’yansa biyu da ’yan uwansa biyu da wani dan dan uwansa da ya ziyarci gidan.
An kuma garzaya da matar gidan da danta daya zuwa asibiti domin ba su kulawar gaggawa a sakamakon ibtila’in na ranar Litinin da dare.
 Jami’in hulda da Jam’a a hukumar kashe Gobara ta Jihar Kano, Sa’idu Muhammad ya ce hukumarsu ba ta samu kira daga unguwar ba, don haka ba su da labarin abin da ya faru.
 Ana ganin yakamata su bincika don sanin lamarin da ake ciki ganin an samu rashin rayukka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *