Spread the love

Sukar  shirinmu na sasanci da ‘yan bindiga ba zai hanamu ci gaba da shi ba—-Gwamna Matawalle.

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammed Matawalle ya bayyana cewa ‘yan siyasar Abuja dake suka ga shirin sulhu da ‘yan bindiga ba zai hana shi cigaba da yin shi ba, domin yaga alfanunsa.

Gwamnan yayi wannan bayani ne yau lokacin da yake karbar makaman wasu ‘yan bindiga da suka tuba kuma suka mika bindiga kirar AK 47 guda biyu da dunbin harsasai ga gwamnatin jihar ta Zamfara.

Matawalle yace, akwai wasu ‘yan siyasar Abuja dake can basu san abin da ke faruwa a jihar su ba don ba su zuwa, amma don dai neman suna sai su tara ‘yan jarida suna ta maganganun banza game da shirin mu na sulhu.

Haka zalika ya ce, idan dai Zamfara ce a gaban su to suzo su bada tasu gudun muwa ta yanda za’a kai karshen wannan matsala data addabi Zamfarawa.

“Wai sai kaga mutun ya koma Abuja yayi kwancin sa bai san abinda ke faruwa ba, amma sai kawai ya sa yara sunata rubuce rubucen banza game da abinda ba yada tabbaci a kansa.

” To mu munada yakini cewa tunda Ubangiji yace ayi sulhu to zamu samu nasara, don wannan shirin a hankali ake tafiya dashi. Yanzu haka akwai wasu yan bindiga da suka yi alkawarin rungumar shirin mu na sulhu, wanda cikin wannan satin zasu kawo makaman su”.inji gwamna.

Hakama yace, bayan sulhun da ake ci gaba dashi kuma ana nan anata karbar makamai garesu, inda wayan nan mutun ukkun sun mika muna bindiga kirar AK 47, guda biyu tare da Harsasai masu yawa.

Da yake yiwa gwamna bayani, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Abubakar Muhammed Dauran yace, bayan wayan nan yanzu haka akwai da zasu kawo makaman su nan gaba kadan, ya kara da cewa insha Allahu wannan gwamnati zata yi nasarar abinda tasa a gaba.

Dauran ya kara da cewa wayanga tubabun yan bindiga sun fito ne daga karamar hukumar mulkin Bakura, kuma sun bada tabbacin cewa ba zasu kara komawa cikin wannan halin da baya da kyau.

Shima a nashi jawabin shugaban tubabbun yan bindigar ,mai suna Amadu yace sun yanke shawarar barin ta’addan cine saboda Allah da kuma ganin adalcin da gwamna Matawalle ke yiwa Fulani a duk fadin jihar.

Yace, amma aja kunnuwan yan sakai dasu daina kashe masu uwaye da kuma kona masu muhalli domin aci gaba da samun zaman lafiya.

Daga karshe dai an basu rantsuwa da Alkur’ani mai tsarki, kuma sun rantse ba za su sake kashe kowa ba, da kuma yin sata da garkuwa da mutane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *