Spread the love

Daga Muhammad M. Nasir.

A ranar Assabar data gabata ne jam’iyar PDP a jihar Sakkwato ta tsayar da dukkan ‘yan takararta da za su waƙilci jam’iyar a zaɓen ƙananan hukumomi da za a gudanar watan Maris mai zuwa.

An tsayar da dukkan kansiloli na mazaɓu da ciyamomi a ƙananan hukumomi 23 na jihar Sakkwato.

Managarciya ta samu bayani  yanda Gwamnan Sakkwato da kansa ya jagoranci fitar da ‘yan takakarar daga  farko harkarshe hankan ne ya jawo hankalin mutane musamman ‘yan siyasa ganin wannan ne karon farko a siyasar jihar, bayan kammalawa ne aka fahimci Tambuwal ya yi haka ne domin ya haifo gidan siyasarsa kamar kowane jagoran siyasa a jihar Sakkwato.

Tambuwal ya mayar da tsoffin ciyamomi biyar a takarar waɗanda suka haɗa da Keɓɓe da Binji da Silame da Sakkwato ta kudu da kuma Gwadabawa, a sauran ƙananan hukumomin ya sanya sabbin fuskoki da yake da yaƙinin shi ne uban gidan siyasarsu in ka cire ƙaramar hukumar Isa da ake zargin tsohon gwamna Attahiru Bafarawa ya yi masa tsaye a takararsa.

Alamu ya nuna Tambuwal ya ɗauko hanyar gina gidan siyasarsa wanda a tsawon lokaci ba ya da shi, yana yin dallo ne a ginin wasu yana kai ga nasara.

Jarman Sakkwato Alhaji Umarun Kwabo A A yana cikin jagororin siyasa a jihar da yake da na shi gidan siyasa kuma yana da tasiri a tsawon lokaci wurin samun nasarar zaɓe, a wannan fitar da ‘yan takarar an yi ta yaɗa jita-jita a gari cewa Jarman Sakkwato ya goyi bayan tsohon shugaban ƙaramar hukuma Alhaji Aminu Ibrahim da aka fi sani da No delay, sai ga shi Tambuwal bai ɗauki zaɓin ba ya yi gaban kansa da fitar wani dattijo Alhaji Mustafa Shehu Sokoto zaɓin da aka yi na’am da shi.

Wannan abin da Gwamna ya yi na kaucewa zaɓin wannan jigon zai yi karya lagon siyasarsa a jiha?

Wasu na da ra’ayin hakan ba zai taɓa siyasar ba domin jarma yana da komi a gwamnatin Tambuwal da suka fi ƙarfin kujerar ciyaman.

Wasu na ganin hakan matsala ce ga siyasarsa musamman maganar 2023 da ake ganin suna da ra’ayin siyasa a lokacin in ya zo.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *