Tsohon gwamnan jihar Imo Sanata Rochas Okorocha an kama shi bayan sabawa dokar gwamnan jiha mai ci Hope Uzodimma in da ya bude hotel dinsa dake kan rukunin gidajen Royal Palm bayan da gwamnatin jiha ta rufe shi.

Yana tare da rakiyar surukinsa Uche Nwosu tsohon gwamnan ya balle makullin da aka garkame wurin domin ya isa  rukunin gidajen da suke mallakin matarsa Nkechi.

A lokacin da yake wannan lamari an samu hatsaniya in da aka yi wa mutum daya rauni.

A jumu’ar data gabata ne gwamnatin jihar ta karbe rukunin gidajen dake saman hanyar Akachi a birnin na Oweri.

An karbe wurin ne karkashin jagorancin kwamishinan filaye kan umarnin rahoton kwamitin korafi da shari’a da aka kafa na a dawo da filayen gwamnati da wasu abubuwan da suka shafi wannan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *