Spread the love

Matar gwamnan jihar Kebbi Dakta Zainab Bagudu ta aurar da ‘yarta Hajiya Aisha Shinkafi Sa’idu ga tsohon kakakin majalisar tarayyar Nijeriya  Dimeji Bankole bayan ya saki tsohuwar matarsa a 2017.

An kamala shagalin bukin da aka yi a watan Junairu amma har yanzu lamarin sabo ne a wurin matar gwamna Bagudu. Tun sanda lamarin ya faru dakyar ka ga ranar da ba ta daura hoton bukin auren a turakarta ta watsAPP status ba.

Tana nuna tsintsar so da farinciki yadda ta shedi shagalin bukin ‘yarta tana raye  amatsayinta na uwa.

Dakta Zainab kwararrar likita ce da ta yi fice a wurin yaki da cutar daji da tauye hakkin yara kanana.

A matsayinta na matar gwamna ta zama abar koyi ga wasu mutane musamman aiyukkan da take yi na wayar da kan jama’a musamman mata da yara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *