Spread the love
Tsaro: Ku Sako Mana ‘Yan Uwa Dan Samun Lafiyar Da Ku Ke Bukata- ‘Yan Bindingan Daji
Daga M. A. Umar, Minna
Maharan ‘yan bindiga sun nemi gwamnatin Neja da ta taimaka masu wajen sakin mambobinsu da jami’an tsaro suka cika hannu da su kuma suke tsare har yanzu a wasu sassan jihar saboda zaman lafiyan ya tabbata.
Wasu daga cikin kwamandojin maharan ne suka bukaci hakan a lokacin da tawagar gwamnatin jihar ta ziyarci sansanin ‘yan bindigar da ke Dutsen Magaji, dan tattaunawa da maharan hayoyin samun zaman lafiya da kawo ƙarshen garkuwa da mutane da faɗan  makiyaya a faɗin jihar bisa jagorancin sakataren gwamnatin jihar, Ahmed Ibrahim Matane.
Tunda farko da yake bayani ga kwamandoji da sauran muƙarraban maharan, sakataren gwamnatin Neja, Ahmed Ibrahim Matane yayi kira ga da su ajiye makaman su kuma su rungumi sulhu dan samun zaman lafiya da tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Sakataren ya bayyana hakan ne Dutsen Magaji cikin ƙaramar hukumar Mariga lokacin da yake bayani ga ‘yan bindigar da kwamandodin su da ke ta’addanci a jihar.
Sakataren wanda ya zuyarci sansanin maharan tare da sanannen malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmed Abubakar Gumi alhamis din makon da ya gabata dan tattaunawa da su akan yawaitar garkuwa da mutane da fadan makiyaya da manoma ta yadda za a samu zaman lafiya ta hanyar sulhu dan kawo ƙarshen matsalolin tsaro da jihar da ba ta san da shi ba tsawon shekaru.
A yunkurin sulhun, Ahmed Matane ya jawo hankalin kwamandojin da su goyawa gwamnati baya wajen sako mutanen da ake garkuwa da su wadanda aka kwashe a motar sufuri mallakin gwamnatin jiha (NSTA) da daliban makarantar kimiyya ta gwamnati da ke Kagara, ya kara da cewar hare-haren kwanakin nan tamkar maarkashiya ce wa zaman lafiya.
Ya bada tabbacin gwamnati za ta cigaba da daukar matakan tsaro dan kare rayuka da dukiyoyin jama’a ta hanyar karfafa guiwar jami’an tsaro a jihar, saboda haka akwai bukatar jama’a da su yi hadin guiwa da gwamnati akan kudurin karya lagon duk wani ta’addanci a jihar.
Sakataren ya nemi malaman addini, shugabanni su rika bada gudunmawar yadda za a samu masu garkuwa da jama’a, makiyaya da masu rigima da manoma ta yadda za a samu cin ma nasarar gwamnati wajen zaman lafiya a jihar.
Da yake karin haske, malamin addinin musuluncin nan mazaunin Kaduna, Sheikh Ahmed Abubakar Gumi, yace matakan yin sulhu da ‘yan bindigar zai bada kofar kawo karshen rashin tsaron da jihar da kasa ke fuskanta gaba daya.
Sheikh Gumi ya jawo hankalin ‘yan bindigar illar kashe rayukan al’umma a musulunci, ya nemi da su rungumi zaman lafiya da ajiye makaman su.
Malamin ya bayyanawa maharan cewar zai cigaba da tuntubar gwamnatin jiha dan samar masu da tallafi da abubuwan da suka bukata, gwamnati za ta ba su tallafin da zai ba su damar cin ma kudurin su na rayuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *