A watan Satumban 2013 daruruwan matan da ba su da aure karkashin jagorancin Suwaiba Isah suka gudanar da zanga-zanga a kan titin Gusau birnin jihar Zamfara kan rashin mazan aure in da yawansu yakai 8000. Haka kuma an gudanar da irin wannan zanga-zagar a Kano karkashin jagorancin Hajiya Altine Abdullahi a Agustan 2009 tsakanin ‘yan mata da zawarawa abin da ya ja hankalin gwamnati ta shirya aurar da mata 1000 a jihar.

Lamarin yana tare da al’ummar Arewa maso gabas ba musulmai kadai ba wani Fasto a jihar Gombe ya nuna damuwarsa ga yanda ake fama da rashin mazajen aure a yankin.

Godiya Adamu mai shekara 35 har yanzu ba ta samu mijin da za ta aura ba, yanayin da ake ganin laifinta, ta ki tsayar da miji ta yi aure.

“Tau ya zan yi? zan matsawa kai na ne wurin mijin da bai zo ba” ta bayyana cewa ta yi hulda da namiji biyar amma duk ba da gaske suke yi ba “abin da kawai na sanya a gaba in yi rayuwata ko ba miji” a cewarta.

Amina bafiltana ce a kalamanta ta ce matsalar da suke fama da ita ta rasa miji karatun da suka yi ne, ta fahimci da yawan maza ba su son mace mai yawan karatu. Domin suna ganin akwai wahala su iya juya wadda take da yawan karatu, ba su da wani zabi kan haka in auren ya zo za a yi in bai zo ba wani batun ta da hankali.

Babban limamen gidan gwamnatin Gombe Shaikh Zakariyya Hajiya ya daura cewa abin da ya sanya aka samu wahalar mazaje ga mata bai fi talauci ba.

Ya ce Sadaki da lefe da kayan kichin da kayan gyara daki da sauransu suna sanya maza ja baya, sai kuma matan yanzu ba su son a yi masu abokiyar zama.

Wani malami yana ganin yanayin rayuwa ne ya sa auren ya yi tsada ga maza ba su da kudi duk yanda aka yi maka rahusa a aure sai ka kashe dubu 200, in za ka yi lefe sai ka kashe dubu 600 ko miliyan daya.

A yanda musulunci ya ce lefe ba zai kasa dubu 25 ba sauran wahalhalun da ake daurawa ne ke sanya aure bayan yinsa ba zai wuce wata shidda ba ka ga an rabu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *