Spread the love
Gaba Kadan Duk Yaron Da Bai Da Rajistan NPopC Ba Zai Shiga Makarantar Boko Ba A Neja
Daga M. A. Umar, Minna
Al’ummomin yankunan karkara sittin ne hukumar wayar da kai ta kasa ( NOA) ta shirya wayar masu da kai kan muhimmancin yiwa yara kanana a jihar Neja. Tunda farko da yake bayani a taron a tattaunawa da al’ummomin karkaran, darakta janar na hukumar NOA, Malam Yahaya Ibrahim Gbongbo, yace sun shirya wannan taron ne da hadin guiwar hukumar kidaya ta kasa (NPopC) da taimakon UNICEF dan wayar da kan al’ummomin yankunan karkara sittin da suka fito yankunan kananan hukumomi shida domin yin gwaji.
Gbongbo, ya cigaba da cewar rajistan zai taimakawa gwamnati wajen samun saukin bada ilimi, kiwon lafiya da kariya ga yara masu tasowa dan tattara kididdiga da gado na dindin din.
Yace kananan hukumomin da zamu fara da su sun hada da karamar hukumar Gbako, Edati da Bosso, Gurara, sai Mariga da Mashegu.
Shirin wanda aka yiwa lakabi da ‘A yiwa yara rajista”, za a fara gudanar da shi ranar talata 23/02/21 wanda zai dauki adadin kwanaki biyar kafin fara karban rajistan.
Hukumar NOA tace a shekarar 2018, yara 43 ne kawai aka yiwa rajista a jihar. Za mu samar da cibiyoyi hudu a kowace karamar hukuma, ta yadda za mu samu saukin isar da sakon ga al’ummomin da abin ya shafa.
Yahaya Gbongbo, yace shirin rijistan yara kananan ya wahalar da gwamnatoci da dama, saboda yadda jama’a ba su fahimci shirin ba, akwai bukatar ilmantar da jama’a dan wayar masu da kai ta yadda zasu samarwa yayansu rajistan, kan haka muka bukaci hukumar UNICEF dan ganin yadda suka dama da bukatun yara.
Kan haka hukumar mu NOA ta hada kai da hukumar kidaya ta kasa dan yin aikin a kananan hukumomi shida dan wayar masu da kai da nuna masu muhimmancin rajistan ta yadda a karshen shirin za a iya yiwa yara dubu arba’in rajista masu shekaru biyar da haihuwa.
Uthman Baba, shi ne shugaban hukumar kidaya ta kasa reshen Neja, yace yiwa yara rajista zai taimaka masu wajen samun takardar shaidar haihuwa, da zai taimaka wa hukumar damar sanya su a cikin kididdigar kasa.
Dan haka hukumar NOA, za ta yawuta wajen da kan jama’a sanin muhimmancin sanya yaran da ake haihuwa cikin kididdigar kasa.
Mista Milfred Mama, shi ne jami’in hukumar UNICEF, yace mun damu ne akan rayuwar yara daga matakin farko har zuwa girmansu, wanda da dama ba sa cikin lissafin kididdigar kasa. Yanzu mun yi hadin guiwa da hukumar NOA da hukumar NPopC ta kasa reshen jihar Neja dan tabbatar da cewar an sanya yara masu shekaru biyar na haihuwa cikin kididdigar kasar nan ta yadda za su samar shiga cikin kasafin kasa har karshen rayuwarsu musamman wajen samar masu da takardar haihuwa da zai ba su damar shiga cikin lissafin kasa.
Uwargidan gwamnan Neja, Dakta Amina Abubakar Sani, da ta samu wakilcin babbar sakatariyar ma’aikatar jin dadin mata da walwala, Madam Kaltumi Dauda, tace wannan shirin za a fara shi ne a matakin wayar da kai, amma zuwa gaba akwai yiwuwar ba wani yaron da zai shiga makarantar gwamnati sai yana da wannan rajistan.
A cewarta yin rajistan zai taimakawa gwamnati wajen ganin ba ta bar kowa a baya ba dangane da kasafinta, wanda zai alfanu matuka wajen samar da ingantacciyar rayuwa ga yara masu tasowa, yanzu za su fara da kananan hukumomi shida, saboda halin matsin tattalin arzikin kasa sauran kananan hukumomi sha tara da suka rage za su biyo baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *