Buhari ya naɗa shugaban civil defence dana gidan yari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa shugaban civil defence na ƙasa kwamanda janar Ahmed Abubakar Audi naɗin ya biyo bayan ritaya da tsohon shugaban Abdullahi Gana Muhammadu ya yi a watan junairu.

Ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbosola ne ya fitar da bayanin ya ce shugaban ƙasa ya kuma aminta da aika sunan Haliru Nababa a matsayin shugaban hukumar gyara halinka wadda aka fi sani da gidan yari.

A bayanin da daraktan ‘yan jarida na ma’aikatar Muhammad Manga ya fitar  ya ce Audi yana kan gaba a cikin waɗan da ma’aikatar ta zaɓa.

Ya ce tura sunan da aka yi a majalisar dattijai an yi haka ne bisa ga tanadin dokar da ta samar da hukumar gidan yari ta ƙasa a shekarar 2019.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *