Spread the love

Tsohon shugaban hukumar Kwastam Dikko Inde ya rasu

Rahotanni daga Abuja sun tabbatar da rasuwar tsohon shugaban hukumar hana fasa ƙwauri ta Nageriya Dikko Abdullahi Inde,

Bayanai sun ce Dikko Inde ya rasu ne a wani asibiti dake Abuja.

An dai haifi Dikko Inde a garin Musawa ta jihar Katsina a shekarar 1960, ya shiga aikin kwastam a shekarar 1988.

Bugu da ƙari an naɗa shi shugaban hukumar kwastan a shekarar 2009, muƙamin da ya riƙe har zuwa watan Agusta 2015.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *