Spread the love

Kungiyar kwadagon jihar Zamfara ta aikawa gwamnatin jiha karkashin jagorancin Muhammad Bello Matawalle takadar  tunatarwa kan mafi karancin albashin 30,000 da har yanzu gwamnatin ba ta aiwatar ba, kuma ba wani labarin ranar fara karbar albashin da sauran jihohi sun dade da aiwatar da nasu.

Tun watan Disamban 2019 aka kafa kwamitin da zai baiwa gwamnati shawara kan karin albashin karkashin Ambasa Bashir Yuguda, kwamitin ya kammala aikinsa ya mika rahoto ga gwamna a watan Okotoban 2020 domin aiwatarwa.

Kungiyar ta nuna rashin jindadinta yanda gwamnati ke jan kafa ga aiwatar da aikin kwamiti wata uku bayan kammalawa, don haka take bukatar gwamna ya bayar da umarni a fara biyan ma’aikatan Zamfara mafi karancin albashi ko yanzu sun yi hakuri sosai.

Takardar wadda shugaban kungiya Kwamared Sani Halliru da sakatarensa suka sanyawa hannu sun nemi gwamnati ta gaggauta fara biyan ma’aikata mafi karancin albashi na 30,000 don haka shi ne yafi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *