Bayan jinkirin kwana 4 APC ta sabunta rijistar Yariman Bakura

Bayan turka turkar kwana hudu tsohon gwamnan jihar Zamfara Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura a jiya ya sabunta katin rijistar jam’iyarsa ta APC .

Akwai wata makarkashiya da ake ganin ana son hanawa tsohon gwamnan kuma sanata karo a uku ya sabunta rijistarsa.

A satin da yagabata an sabuntawa shugabannin APC a jihar Zamfara rijistarsu aka ketare Yarima.

Yariman Bakura an sabunta rijstarsa a garin Gusau bayan shigar fadar shugaban kasa da wasu gwamnoni.

Na kusa da Yariman Bakura Junaidu Dosara ya dora laifin jinkirin ga shugabannin APC a Zamfara.

Dosara ya godewa shugaba Buhari da wasu gwamnoni da suka shiga cikin lamarin aka sulhunta, za su yi aiki tukuru APC ta samu nasara a dukkan matakai.

Shugaban kwamitin kula da rijistar  a Arewa maso Yamma Sanata Abba Ali yana cikin wadanda suka shedi bayar da rijistar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *