Spread the love
Daga M. A. Umar Minna
Mahara sun auka kwalejin fasaha ( GSS) Kagara a daren jiya inda suka yi awon gaba da ɗalibai da malaman su tare da kashe wasu daliban uku.
Ɗaya daga cikin waɗanda abin ya rutsa da shi kuma ya samu kuɓuta yace maharan sun shigo rukunin gidajen malamai ɗauke da muggan makamai daga nan suka nosa wurin kwanan ɗalibai da misalin ƙarfe biyu na dare.
Malam Batagi da ya samu kuɓuta daga hannun maharan yace maharan sun yi awon gaba da Malam Lawal, Ali da Hannatu da mijinta, da Malam Dodo da kuma Malam Muhammed Abubakar ( Akawu) da kuma wasu da ba a tantance ba zuwa yanzu.
Maharan dai sun kashe ɗalibai uku ta hanyar harbi da bindiga nan ta ke waɗanda yanzu haka an garzaya da gawarwakin su zuwa babban asibitin gwamnati da ke garin Kagara.
Ko a daren talata dai maharan sun auka garin Zara da ke yankin Kusharki a ƙaramar hukumar ta Rafin inda suka kashe sarkin garin da wasu mutane biyu.
Ƙaramar hukumar Rafi da ke iyaka da jihar Kaduna ta daɗe tana fama da hare-haren maharan wanda ya kai ga kashe dagacin Madaka tare da kashe shi bayan tsawon lokacin da ya ɗauka hannun maharan, sai dagacin Gunna da ke hannun maharan da zuwa yanzu ya kwashe sama da wata biyu a hannun maharan ba ɗuriyarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *