Ahmad Lawan Yayi Allah Wadai da sace daliban Makarantar Kagara tare neman Kakaba dokar tabaci kan Matsalar Tsaro
Daga M. A. Umar
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan yayi Allah wadai da harin da yan bindiga suka kaima makarantar sakandiren gwamnati ta kimiyxa dake Kagara a jihar Niger a inda aka sace wasu daga cikin dalibai da malaman makarantar.
Ola Awoniyi da Ezeil Tabiowo masu taimakawa shugaban majalisar bangaren yada labarai ne ya fitar da sanarwar larabar nan ga manema labarai.
Lawan ya bayyana harin na daren ranar Laraba a matsayin muganta kuma mummunan laifi, inda yayi kira ga jami’an tsaro su tabbatar sun ceto mutanen da kuma kama yan bindigar.
Yace, “ya kamata jami’an tsaron mu su hada hannu a tsakanin su da gwamnatin jihar domin samun nasara.
“Ya zama wajibi ga gwamnatoci a dukkan matakai su tabbatar daga yanzu an bada cikakkiyar kariya ga  makarantun mu daga harin wadannan marasa imanin da suka mai da makarantu abin saukin kai ma hari”.
Shugaban majalisar ya jajanta ma iyali da iyalan daliban da malaman da aka sace da kuma gwamnati da jama’ar jihar Neja
Ya kuma tabbatar ma yan Najeriya da shirin majalisar dattawa ta yi aiki kafada da kafada da gwamnatin tarayya domin shawo kan rashin tsaro a Najeriya.
Haka kuma majalisar dattawan ta bukaci shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kaddamar da dokar ta baci a harkar tsaro cikin gaugawa.
Majalisar ta yi Allah wadai da kakkausar murya sace dalibai da malaman makarantar sakandire ta kimiyya dake Kagara, jihar Niger.
Majalisar ta cin ma wannnan kudurin ne bayan ta yi nazari da amincewa da kudurin da Sanata Sani Musa (APC-Niger) ya gabatar mata.
Sanata Musa yayi bayanin cewa wasu yan bindiga cikin kakin soja suka kai hari a makarantar da asubahin ranar Laraba inda suka ci karfin masu gadin suka kwashe daliban da malaman, bayan su  kashe wasu da har ya zuwa lokacin ba’a san adadin su ba.
Sace daliban, a cewar Sanatan ya faru yan kwananki bayan sace dalibai 300 na makarantar sakandiren gwamnati ta Kankara, da sace dalibai 100 na makarantar yan mata dake Dapchi a 2014, jihar Yobe.
Ya nuna damuwarsa cewa jihohin Niger, Katsina da wasu jihohin a arewa maso yamma, da na arewa ta tsakiya suna fama da matsalar harin yan bindiga dake kashewa da sace mutane duk da yawan yan sanda da sojoji da aka zuba.
Yace ko a ranar Lahadin da ta gabata an sace fasinjoji 54 a hanyar Kundu wadanda har zuwa yau ba a sako su ba.
Bayan tattaunawar, majalisar ta bukaci shugaba Buhari da ya aiwatar da rahoton kwamitin majilsar akan tsaro da ya kunshi dukkanin hanyoyin da za’a bi don shawo kan matsalar rashin tsaro.
A jawabin sa, shugaban majalisar, Ahmad Lawan ya jaddada muhimmancin bukatar hada hannu tsakanin sojoji da sauran jami’an tsaro da gwamnatocin jihohi don samar da tsaro a makarantun da ke arewacin Najeriya.
Yace mafi yawancin satar dalibai yafi faruwa a arewacin Najeriya  abinda ke neman kawo koma baya ga kokarin shuwagabannin baya na tabbatar da ganin yaran arewa sun shiga makarantar boko.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *