Spread the love

Da yawan mutanen Arewa dake zaune a jijar Oyo sun dawo Arewa bayan rikicin da ya ɓarke tsakanin Hausawa da Yarbawa a kasuwae Shasa cikin garin Ibadan a satin da ya gabata.

Wasu daga cikin mutanen Arewa da suka bar unguwanninsu tsakanin Jumu’a da Assabar sun ce sai da suka riƙa baiwa jami’an tsaro kuɗi daga dubu biyar zuwa 10  su raka su zuwa in da za su tsira, har da zuwa gidan Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyashi.

Ɗaya daga cikin wanda suka tsira ya ce sai da ya biya kuɗi aka tseratar da shi.

In kana iya tunawa rikici ne ya ɓarke tsakanin ƙabilun biyu a ranar Alhamis data gabata har ya kai Jumu’a abin da ya yi sanadin mutuwar kusan mutum 30.

A kasuwar shasa akwai shagunan Hausawa da Yarbawa ababen hawa da yawan gidaje aka ƙone a rikicin.

Wasu daga cikin mutanen da suka bar Ibadan sun yi haka ne domin sun yi hasarar kayansu gaba ɗaya shaguna da gidaje kuma ba wani tallafi daga gwamnatin jiha da tarayya, sun fara komawa Arewa da mata da yara.

Da yawan mutanen Arewa da ke dawowa suna tafiya Sakkwato da Kano da Kebbi da Kaduna da Jigawa da sauran jihohi, kusan mutum 500 ke gudun hijira a babban garejin Akinyele. Mai garejin Alhaji Yaro Abubakar ya ce matasan da ke wurinsa suna nan tun ranar Jumu’a yayinda wasu suka sulale zuwa gidajensu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *