Spread the love

Ana hasashen litar man Fetur a Nijeriya za ta koma 190 domin gangar danyen man fetur farashinta a yanzu ya koma dala 63 ga kowace ganga.

Masu ruwa da tsaki a kan harkar man fetur a Nijeriya suna aiki ba dare ba rana domin fitar da sabon tsarin sayar da litar man fetur saboda gangar danyen man ta tashi a duniya a jiya Littinin.

Kafin wannan  litar man fetur ana sayar da ita tsakanin naira 159 zuwa 165 amma yanzu akwai yiwuwar za ta koma 190 a wadan nan kwanaki masu zuwa.

Kudin dakon man ya tashi daga 151 a kowace litar man zuwa 180, saboda gangar danyen man ta koma dala 63 a kasuwar duniya a ranar litinin.

Gangar Man farashinta ya daga daga $58 zuwa $63 hakan ke nuna  matatun man za su karawa kwastomominsu kudi.

A satin da ya gabata Ministan Man fetur Timipre Sylva ya sanarwa mutanen Nijeriya su shiryawa daukar dafin  da ke tafe na karin kudin man fetur.

Managarciya ta fahimci tun da an cire tallafin man fetur ga mutanen kasa za su cigaba da shan ukuba kenan duk sanda farashin gangar mai ta daga suma za su ji a jikinsu, arzikin man fetur zai cigaba da amfanar wasu tsirarun mutane kenan ba duka mutanen kasa ba.

Hakan ya nuna tashi gangar danyen man fetur murna ce ga masu mulkin Nijeriya, bakin ciki ne ga talakan kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *