Rigimar Ibadan: An binne mutum 20, yayinda 5000 ke gudun hijira

Akalla mutum 11 aka yi wa sutura a ranar Lahadi bayan rikicin Hausawa da Yarbawa ‘yan kasuwa da ya barke a kasuwar Shasa a karamar hukumar AKinyele a jihar Oyo.

Haka kuma kusan mutum 5000 Hausawa masu kasuwanci mata da yara ke gudun hijira a gidan Sarkin Shasa Alhaji Haruna Maiyasin da hukumar kula da Noma(IITA) dake Ibadan, bayan rikicin.

Sarkin Shasa a zantwarsa da daily trust ya ce a gidansa mutum 11 aka yi wa sutura. Amma wata majiyar ta ce a al’ummar Hausawa an kashe mutum 20 dukansu an binne su a Makabartar Akinyele  a birnin jihar.

Wasu miutum 8 da aka kashe a lokacin rikicin suna a ofishin ‘yan sanda dake Shasa a ranar Lahadi da marece.

Akinyemi Kazeem ya dora laifin lamarin ga rashin kyakkyawan shugabanci, lamarin ya fara tun ranar Alhamis ba wani kyakkyawan mataki da aka dauka.

Haruna Baba ya ce mutum 5000 da aka ce suna gudun hijira haka ne ga wanda ya fada maka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *