Spread the love

 

 

Daga Muhammad M. Nasir.

Jam’iyar APC a jihar Zamfara ta hanawa tsohon gwamnan jihar na farar hula Sanata Ahmad Yariman Bakura katin jam’iya.

Sanata ya tafi mahaifarsa a karamar hukumar Bakura da safen ranar assabar da nufin karbar katin  domin ya sabunta rijistar jam’iyarsa, tun  da safe yake jiran jami’an da ke raba katin su zo ya karba amma shiru kake ji har zuwa 10 na daren ranar sai suka aiko masa da ya koma birnin Gusau za su kawo masa haka an ka yi ya tafi amma ba su ba shi katain ba.

Daga baya aka nadi wani sautin muryar jigo a jam’iyar APC a karamar hukumar Bakura Alhaji Bello Dankande Gamji yana fadin Yarima ba dan jam’iyarsu ba ne don haka ba za su bashi kati ba.

“Sanata ya yi taro jiya yana da hakki ya yi taro a karamar hukumar domin ya tallata ra’ayinsa ga mutane, mu ba mu dauki taron APC ne aka yi ba, ya tara mutanen PDP don ya nunawa duniya mutanensa, amma taron APC ba ne, balle har mu yi tuananin zuwa taron.” a cewarsa.

Ɗankande ya ci gaba da cewa wanda ke APC shi za a ba kati babu in da Yarima zai fito ya ce yana APC shi ba ɗan jam’iyar ba ne in yana so ya je ya yi wanka don shi ɗan PDP ne mun bar shi yayi ra’ayinsa.

“Ba za mu bashi kati ba sai mun yi mashi wanka ya fito ya faɗawa duniya ya bar PDP, don a halin da ake ciki ba APC yake ba in ko ita yake ya fito ya faɗi gudunmuwar da ya bayar na ci gaban jam’iya.

Managarciya ta yi yunƙurin jin ta bakin Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura amma abin ya faskara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *